Kwarin da ake iya ci za su taimaka wajen yaki da yunwa

Kwarin da ake ci a cikin faranti
Image caption FAO ta ce za a yi amfani da kwari a matsayin abinci a nan gaba

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya yi bayani game da muhimmiyar rawar da kwarin da aka iya ci zasu taka wajen yaki da yunwa a duniya.

Hukumar samar da abinci da ayyukan noma ta duniya, FAO, ta ce akwai mutane biliyan biyu da tuni suke cin kwari irin su gyare da fari da kuma shinge a matsayin abinci.

Wata mai magana da yawun Hukumar ta FAO, Afton Halloran, ta ce akwai yiwuwar a yi matukar amfani da kwari nan gaba a matsayin abincin dabbobi da kuma na bil'adama.

Sai dai rahoton na cewa kyamar da wasu ke nunawa , musamman a kasashen yammacin duniya ga irin wadannan kwari, shi ne abin da zai yi tarnaki ga yaduwar amfani da su.

Karin bayani