Mahaukata sun tsere daga asibiti a Nairobi

Kenya
Image caption Wata mara lafiya a asibiti

'Yan sanda a kasar Kenya sun ce, masu tabin hankali 41 ne suka tsere daga asibitin da ake kula da su na Mathari da ke Nairobi babban birnin kasar.

Jami'an 'yan sandan sun shaida wa BBC cewa, an kaddamar da wani bincike a kan masu tabin hankalin, wanda yawancin su haukar ta su ta kai ga duka.

Jaridar standard ta Kenya ta rawaito cewa, mahaukatan sun tsere asibitin ne bayan sun yi korafin cewa magungunan da ake basu basu da inganci.

Asibitin na Mathari dai shi ne babban asibitin masu tabin hankali a Kenya.

A shekarar 2011, kungiyoyin kare hakkin dan-adam sun yi kira da a gudanar da bincike a kan abin da ake zargi na take hakkin dan adam da ake yi a asibitin.

Wani babban jami'in 'yan sanda a Nairobi, Moses Ombati ya shaida wa BBC cewa, masu tabin hankalin sai da suka gudanar da zanga-zanga kafin daga baya su fi karfin masu gadin su tsere.

Jami'in ya ce yanzu haka suna da hotunan wadanda suka tseren ta yadda neman su zai zo musu da sauki.