Amurka da Burtaniya za su kara matsa lamba a kan Assad

Mr Obama da Mr Cameron
Image caption Mr Obama da Mr Cameron

Shugaba Obama ya ce Amurka da Birtaniya sun amince su kara matsa lamba ga gwamnatin Syria don ta amince da wata gwamnati ta gaba,ba tare da Shugaba Bashar al-Assad ba.

Shugaba Obama ya kuma shaidawa manema labaru a Washington cewa kasashen biyu za su yi aiki tare da wakilan gwamnatin Syrian da kuma na 'yan adawa game da wani taron sulhu da za a gudanar cikin makonni masu zuwa a Geneva.

Ya bayyana haka ne bayan wasu shawarwari da Firayim ministan Birtaniya David Cameron, wanda ke cewa Birtaniya za ta nemi tarayyar Turai ta kara sassauta haramcin shigar da makamai cikin Syria.

Karin bayani