An cire wa Angelina Jolie nono don gujewa cutar sankara

Angelina Jolie
Image caption Tauraruwar fina finai Angelina Jolie

Tauraruwar finafinan Holywood, Angelina Jolie ta bayanna cewa ta sa an cire ma ta dukkan nononta na hagu da na dama, domin kauce ma hadarin kamuwa da cutar sankarar nono.

A wata kasida da ta rubuta a jaridar New York Times, Ms Jolie ta ce ta yanke shawarar sa a cire ma ta nonon ne saboda tana dauke da wata kwayar halitta mai nakasu, wadda ta sa ta cikin hadarin kamuwa da cutar cancer ta nono, wadda ta zamo ajalin mahaifiyarta, da kusan kashi casa'in cikin dari.

Gareth Evans wani kwararre kan kwayoyin halitta, ya ce , akwai wasu kwayoyin halitta na BRCA 1 da BRCA 2, dake nufin cancer nono ta daya da ta biyu, sune kuma ke kan gaba wajen haddasa cutar sankarar nono.

Angelina Jolie ta ce a yanzu za ta iya ce wa 'ya'yanta su sakata su wala, ba tare da fargabar za su rasa ta ba a dalilin wannan cuta.