An taru a Brussels don taimakawa Mali

Dioncounda Traoré da José Manuel Barroso
Image caption Shugaban Dioncounda Traoré na Mali da José Manuel Barroso, Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai

Daruruwan wakilai daga kasashe da kungiyoyin duniya daban-daban sun hallara a Brussels don halartar wani babban taro da nufin tara gudunmawa ga Mali.

Taron dai na fatan tara fiye da dala biliyan biyu da miliyan dari biyar don taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar da daidaita dimokuradiyyar kasar.

Kungiyar ba da agaji ta Oxfam ta yi gargadin cewa ana bukatar samar da kudade har na tsawon shekaru goma sha biyar don samun sakamako mai dorewa.

Ana sa ran gudanar da zabubbuka a kasar ta Mali a watan Yuli—a karo na farko tun bayan juyin mulkin da aka yi a 2012 wanda ya kai ga masu tsattsauran ra'ayin Musulunci suka kwace iko da rabin kasar.

Daga bisani ne dai dakarun Faransa suka jagoranci yunkurin kwato arewacin kasar daga 'yan tawayen.

Karin bayani