Jami'an Turai sun kai samame a wasu kamfanonin mai

Jami'ai daga tarayyar Turai sun kai samame ofisoshin wasu manyan kampanonin mai a matsayin wani bangare na binciken da ake gudanarwa kan zargin almundahana kan tsayar da farashin mai.

Kampaninin da aka kai wa irin wannan samame sun hada da Shell da BP da kuma Statoil na kasar Norway.

Hukumar tarayyar Turan ta ce akwai damuwar da ake da ita cewa mai yiwuwa sun hada baki wajen sauya wasu muhimman alkaluma, ciki har da wadanda ake amfani da su wajen lissafin abinda magidanta ke kashewa kan makamashi.

Binciken ya biyo bayan irin matakin da hukumomin kudi suka dauka kan wasu manyan bankuna bisa zargin yin coge wajen tsayar da kudaden ruwa.