Pakistan: Nawaz Sharif zai kafa gwamnati

Nawaz Sharif
Image caption Sakamakon zaben Pakistan ya nuna cewa Nawaz Sharif zai iya kafa gwamnati

Sakamakon zaben da aka gudanar a Pakistan ya tabbatar da cewa tsohon Firayim Minista Nawaz Sharif zai iya kafa gwamnati ba tare da ya nemi goyon bayan ko wacce jam'iyya ba.

Sakamakon ya nuna cewa jam'iyyar Mista Sharif ta masu matsakaicin ra'ayin mazan jiya ta lashe kujeru dari da ashirin da uku a cikin kujeru dari biyu da saba'in da biyu na majalisar dokokin kasar, duk da cewa akwai wasu kujerun 'yan kadan da ba a bayyana wanda ya lashe su ba.

Masu sa-ido sun ce idan 'yan majalisa ashirin da biyar din da aka zaba zuwa yanzu a karkashin indifenda suka rike al'adar nan ta marawa jam'iyya mafi girma baya, to jam'iyyar Mista Sharif za ta iya samun yawan kuri'un da take bukata a majalisa ta yi mulki ita kadai.

Sakamakon dai ya nuna cewa jam'iyyar PPP mai barin gadon mulki ta lashe kujeru talatin da daya, yayin da jam'iyyar Tehreek-e-Insaf ta dan wasan Kurket Imran Khan ta zo ta uku da kujeru ashirin da shida.

Karin bayani