Rasha ta kori jami'in jakadancin Amurka

lavrov
Image caption Ministan harkokin wajen Rasha, Sergie Lavrov

Rasha ta bada umurnin a kori wani jami'in jakadancin Amurka a Masko, wanda take zargi da ayyukan leken asiri.

Hukumar tsaro ta tarayya a kasar Rasha ta ce ta kama mutumin ne mai suna Ryan Fogle, yana kokarin daukar wani jami'in leken asirin Rashar domin yayi masu aiki.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Rasha ya ce irin wadannan abubuwa ne da suka rika faruwa zamanin yakin cacar-baki, kuma yana hana yarda da juna.

Gidan Talabijin na Rasha ya nuna hoton wannan mutum da aka ce Mr Fogle din ne sanye da hular gashi, lokacin da ake tasa keyarsa.

Sauran kayayyakin da hukumar tsaron ta kama sun hada da wata taswira, da na'urar gano alkibla, da kuma takardun kudi.