Hoton bidiyo daga Syria na shan suka

Wasu daga cikin sojoji 'yan tawaye a Syria
Image caption Wasu daga cikin sojoji 'yan tawaye a Syria

Wani hoton bidiyo da aka sanya a intanet daga Syria, wanda wani wakilin BBC ya ce ba a taba nuna bidiyo mai muni kamarsa ba tun da aka fara rikici shekaru biyu da suka gabata, ya sha kakkausar suka.

Bidiyon dai ya nuna wani mutum ne da aka ce kwamandan 'yan tawaye ne ya yanko zuciya da hantar wani sojan gwamnati wanda ya mutu sannan ya sa a baki ya tauna.

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta ce wajibi ne a gurfanar da duk wanda ya aikata laifuffukan yaki a gaban kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya; ita kuma gamayyar kungiyoyin 'yan adawa ta ce za a gurfanar da wanda ya aikata laifin a gaban kuliya.

Wakilin BBC ya ce hoton bidiyon ya yi mummunar illa a siyasance ga 'yan adawar kasar ta Syria, kasancewar ya zo ne a daidai lokacin da Amurka da wadansu kasashen ke duba yiwuwar baiwa 'yan tawayen makamai.

Karin bayani