Delta: An tattauna da Fulani

A Najeriya, gwamnatin jihar Delta ta yi barazanar ɗaukar tsattsauran mataki, muddin makiyayan da ke zaune a jihar ba su magance ta'adin kayan amfanin gona da ake zargin dabbobinsu suna yi ba.

Wannan batu ya zo ne 'yan kwanaki kaɗan bayan da gwamnatin jihar ta sanar da matakin dakatar da sababbin baƙin makiyaya daga shiga cikin jihar, a matsayin wani mataki na sa ido kan sha'anin tsaro a sassan jihar.

Koda a wasu jihohin Najeriya dai ana samun takun saƙa tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma.

Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro a sassa daban daban na kasar.