Nijar: An yi alƙawarin daina kaciyar mata

A jamhuriyar Nijar yau ne wasu al'umomin garuruwa ashirin na ƙaramar hukumar Makalondi cikin jahar Tillabery suka ɗau alƙawalin ba za su kara yi wa 'ya 'yansu mata kaciya ba.

Waɗannan al'ummomin sun ce sun ɗauki wannan matakin ne bayan gamsuwar da suka yi da hasken da wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da ma hukumomin gwamnati suka ba su a kan illolin da ke tattare da al'adar yi ma matan kaciya.

Wasu dai na kallon yiwa mata kaciya a matsayin wani nau'i na keta haƙƙin ɗan Adam.

Gwamnatin ƙasar ta Nijar ce tare da haddin gwiwar ƙungiyar UNICEF da CONIPRAT da ke yaƙi da yi wa matan kaciya suka shirya bikin a garin Makalondi, yankin da al'adar ta fi ko'ina ƙamari.