An kubutar da 'yanmata 6 masu ciki a Najeriya

Yansandan Najeriya
Image caption Yansandan Najeriya

'Yansanda a Najeriya sun ce sun kubutar da wasu 'yan mata shidda da aka yi ma ciki daga wasu masu safarar mutane da suke da niyyar sayar da jariransu.

Wani kakakin 'yan sanda a birnin Enugu ya ce an dauke yaran ne daga gidajen iyayensu aka mayar da su wani gidan da ya kira , masana'antar samar da jarirai, inda zasu haihu.

Ana cewa an yi ma 'yan matan alkawarin sayen jariran nasu.

Kakakin 'yan sandan ya ce an shaida masu cewa ana irin wannan safara a birnin na Enugu.

Ko a makon jiya, an kubutar da wasu 'yan matan su sha bakwai, da wasu jarirai goma sha daya, daga wani gidan na samar da jarirai.