Najeriya: Sojoji sun fara kai farmakin kwato iko

Sojojin Najeriya
Image caption Sojojin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojoji fiye da dubu biyu sun fara kaddamar da farmaki dan kwato wuraren da masu gwagwarmayar Islama suka kwace a garuruwan da ke arewa maso gabashin kasar.

Wata majiya daga rundunar Sojin ta shaidawa manema labarai cewa, tuni wasu daga cikin sojojin suka kai hari a sansanonin da ke wani gandun daji.

Kwana biyu dai bayan kafa dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, hukumomi a yau sun yi shelar saka dokar hana fitar dare a Jihar Adamawa.

Rundunar soji ta umurci jama'ar jihar da su zauna a gidajensu daga karfe shidda na yamma zuwa shidda na safe.

Kawo yanzu dai mutane na gudanar da harkokinsu na yau da kullum a Yola, fadar gwamnatin jihar, babu kuma alamar baza sojoji a birnin.

Amma wasu mazauna birnin sun ce sun ga jiragen yaki suna sauka da tashi daga birnin.