Google zai fara sayar da kade-kade

Taron shekara-shekara na Google
Image caption Taron shekara-shekara na Google

Shafin matambayi baya bata, na Google ya bayyana cewa zai fara sayar da kade-kade ga masu hulda da shi.

Shafin ya bayyana hakan ne a taron da yake gudanarwa shekara-shekara. Shafin ya ce zai kaddamar da abin da ya kira Google Play Music all Access a Turance a Amurka a kan dala 10 a duk wata, kuma zai sanya kade-kade kamar Spotifty da Xbox.

Shafin ya kuma ba da sanarwar cewa zai ba su damar binciko muryoyi a manhamar Chrome browser, da kuma masarrafar Google hangouts ta wayoyin salula, wadanda za su ba masu hulda da shi damar yin hira ta video, da aikewa da sakonnin kan-ta-kwana, da kuma musayar hotuna tsakanin Android da Iphones, da ma Chrome.

Shi kuwa, kamfanin da ke yin wayar Blackberry cewa ya yi zai bunkasa yadda yake aikewa da sako a bazarar da ke tafe, inda zai sanya a wasu wayoyin hannu.

Sabbin hanyoyin bunkasa aikewa da sakonnin da kamfanin zai samar sun hada da rarraba fuskar wayar ta yadda za a rika ganin bangarori a lokaci guda,da yin hira ta video, da kuma ta murya za su zo nan gaba a wannan shekarar.

Wadansu masu sharhi na kallon wannan mataki da BB ya dauka na komawa kan Android da iphoneS a matsayin wata hanya da zai fadada al'amuransa. Sai dai zai fuskanci kalubale daga abokan gogayyarsa musamman daga Google handouts da Skype, da What's App , wadanda ke sarrafa sakonni kusan biliyan 20 billiona kowacce rana.

Shafin internet na Amazon kuma ya kaddamar da shirin sa na Coins wato kudin wayar iska wanda ya sanar a farkon shekarar nan. A karon farko a Amurka kawai za a iya amfani da tsarin.

Idan an kaddamar da shirin Amazon, zai bada kyautar kudin coins 500, wato kwatankwacin dalar Amurka biyar ga duk wanda ya mallaki Kindle fire.

A halin da ake ciki, za'a iya amfani da kudin na Coin ne dan siyan Manhajar wasanni, kudin ya bi sahun sauran kudaden internet wadanda suka hadar da Facebook credits da kuma Manhajar xbox points.

A karshe, shafin Bing na microsoft ya shiga inda babu wani shafin fassara ya taba shiga ta hanyar kara Klingon a cikin jerin harsunan da yake fassarawa.

Daga yanzu za'a iya fassara kowanne daga cikin harsunan Bing 41 zuwa harshen da akayi amfani da shi a fina-finan star trek.

Shirin na hadin gwiwa ne tsakanin Bing da masu bincike na Cibiyar Harshen Klingon, wadanda suka yi ta aiki ba dare ba rana tun daga shekarun 1960 da fadada fahimtar harshen.

Karin bayani