Najeriya: An kai hari a garin Daura

Jami'an 'yansandan Najeriya
Image caption Jami'an 'yansandan Najeriya

An shafe kusan daren jiya ana tada bama-bamai da harbe-harben bindigogi a garin Daura na jihar Katsina, arewacin Najeriya

Rahotanni sun ce an fara jin karar bama-baman ne da misalin karfe tara da rabi na daren jiyan a yankin da ofishin 'yan sanda na garin yake, daga bisani kuma ya yadu zuwa sashen da bankuna suke.

Babu dai wasu bayanai na wadanda suka kai wadannan hare-hare, amma wasu mazauna birnin sun ce suna cikin matukar tashin hankali don ba su taba gani ko jin lamari irin wannan ba

A lokacinda aka fara tada bama-baman da jin kaarar bindigogin an samu yamutsi a birnin na Daura, mutane da dama saboda kidima sun shiga daji wasu kuma sun shiga gidajensu sun kulle.