Dokar kare hakkin mata a Afghanistan

Mata a Afghanistan
Image caption Afghanistan ta yi kaurin suna wurin cece-kuce kan batun mata

Ana gab da yin muhawara akan wani kudurin doka akan cin zarafin mata a majalisar dokin Afghanistan, inda magoya bayan dokar ke korafi game da hanyoyin da ake bi wajen aiwatar da ita.

Tuni dai aka amince da dokar amma ta hanyar kudirin shugaban kasa kawai, kuma masu fafutukar kare hakkin mata suna nuna shakkun cewa dokar ka iya shan kasa a majalisar.

Ko kuma a rage mata karfi ta yadda matan za su rasa kariyar da suke da ita a yanzu.

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai, ya sanya hannu kan dokar da ke hana cin zarafin mata, da aurar da kananan yara da ma auren dole, ba tare da amincewar majalisar dokoki ba shekaru hudu da suka gabata.

An dai daure jama'a da dama karkashin wannan doka, sai dai wata fitacciyar 'yar majalisar dokoki Fawzia Koofi, na son a kara wa dokar karfi ta hanyar amincewa da ita a majalisar:

"Babu tabbas kan cewa kowanne shugaban Afghanistan zai mayar da hankali kan batun kare hakkin mata ko kuma ma wannan dokar," a cewarta.

Sai dai da dama daga cikin fitattun 'yan fafutukar kare hakkin mata na ganin matakin ka iya sa su rasa dan gatan da dokar ta tanadar musu.

Saboda mai yiwuwa masu ra'ayin 'yan mazan jiya a majalisar su rage karfin dokar ko ma su yi watsi da ita baki daya.

A lokacin baya da aka taso da batun kare hakkin mata a majalisar dokokin kasar dai, an baiwa hammata iska a lokacin da masu ra'ayin 'yan mazan jiya suka yi kokarin hana sauye-sauyen da aka yi niyyar gabatarwa.

Karin bayani