Azbinawa 'yan tawaye sun gwabza da Larabawa a Mali

Dakarun Mali da na Faransa
Image caption Dakarun Mali da na Faransa

Fada ya barke a arewacin kasar Mali tsakanin kungiyar 'yan tawaye ta galibi Azbinawa, da wata kungiyar Larabawa mai gwagwarmaya da makamai a yankin.

Wani mai magana da yawun kungiyar MNLA , Moussa Ag Assarid ya ce wasu mayaka 'yan kishin Islama ne suka kai hari a kan dakarunsu a garin Anefis, kuma ana ci gaba da tashin hankalin.

Masu aiko da rahotanni na cewa tashin hankalin dake faruwa ya nuna irin yadda mayakan wadanda suka tsere wa hare haren da Faransa ta jagoranci kaddamarwa a kansu da kuma Azbinawa 'yan tawaye, na tsawon watanni hudu, ke ci gaba da kawo cikas a yunkurinta na dawo da zaman lafiya a Mali, gabanin zaben da za a gudanar cikin watan Yuli.