Facebook a kasuwannin shunku - me ya sauya?

Facebook
Image caption Manyan kamfanoni da kungiyoyi duka na amfani da shafin Facebook

Shafun sada zumunta na Facebook yana bikin cika shekara guda da fara sayar da hannayen jarinsa, bayan da aka fara tallata shi a kasuwar shunku ta birnin New York.

Kusan mutan daya daga cikin kowanne mutane goma na al'ummar duniya na amfani da shafin a kowacce rana domin sada zumunta da 'yan uwa da abokan arziki.

Sai dai har yanzu ana nuna shakku kan yadda kamfanin Facebook zai iya amfana da wannan farin jinin na sa domin samun riba.

Shekara guda iwar haka, mutumin da ya kafa shafin Facebook Mark Zuckerberg, ya kaddamar da fara sayar da hannayen jarin kamfanin a gaban ma'aikatansa da ke cike da alfahari.

Inda ya ce: "Wannan wata babbar rana ce a wurinmu. Ku ci gaba da mayar da hankali tare da kara fadada ayyukanku."

Hakika wannan babbar nasara ce, kamfanin da dalibai suka kafa a jami'a shekaru takwas kacal da suka gabata, ya bunkasa, inda darajar hannayen jarinsa ta zarta na manyan kamfanoni kamar Disney da Boeing.

...zai bugi kirji...

Sai dai tauraruwar ta yi saurin dusashewa.

Nan take darajar hannayen jarin ta fadi da kusan rabi, sakamakon shakkun da aka nuna kan yadda kamfanin zai iya samun kazamar riba ta hanyar abubuwan da yake samarwa na kyauta.

Akwai kuma damuwa kan yadda masu amfani da shafin ke kara karkata ga wayoyin salula na tafi-da-gidanka maimakon kwamfiyuta.

Samar da tallace-tallace na da wuya a wayoyin salula saboda rashin girman waya.

Baya ga haka Facebook, na fuskantar kalubale daga sauran shafukan sada zumunta kamar Twitter da WhatsApp.

Benedict Evans mai sharhi kan al'amuran na Enders Analysis, ya ce Facebook ba zai samu tagomashi a wayoyin salula kamar wanda ya samu a kwamfiyuta ba:

Sai dai Facebook na da abubuwan da zai bugi kirji - darajar hannayen jarinsa ta dan farfado.

Kuma kashi 30 cikin dari na kudaden tallace-tallacen da ya ke samu na zuwa ne daga wayoyin salula.

Yayin da adadin masu amfani da shafin ke karuwa - mutane biliyan daya da miliyan dari ne ke amfani da shafin, fiye da mutum daya a cikin kowanne mutane bakwai na al'ummar duniya kenan.

Karin bayani