Hare hare na karuwa a Iraki

Wani wuri da aka kai hari a Iraki
Image caption Wani wuri da aka kai hari a Iraki

An shafe kwanaki hudu a jere ana kai munanan hare hare a wasu yankuna na kasar Iraki, inda aka kashe mutane akalla bakwai.

A daya daga cikin hare haren mafiya muni, 'yan bindiga sun kutsa kai cikin gidan wani jami'in 'yan sanda na rundunar yaki da ayyukan ta'adanci a Bagadaza, inda suka kashe mutane biyar ciki har da jami'in, da kuma iyalinsa, lokacin da suke barci.

A jiya, Juma'a, mutane akalla sittin suka mutu a wasu hare hare bamabamai uku a unguwannin 'yan Sunni a ciki da wajen Bagadaza.

Hare haren sun biyo bayan kwanaki biyu da aka kwashe ana kai munanan hare hare kan 'yan Shi'a a kasar ta Iraki.

Karin bayani