An nemi a halatta shan wiwi

marijuana
Image caption Ana amfani da tabar wiwi sosai a yankin Latin Amurka da ma sauran sassan duniya

Wani rahoto da kungiyar kasashen yankin Amurka ta fitar a kan matsalar haramtattun kwayoyi ta yi kira da ayi duba sosai kan halatta shan tabar wiwi a duniya.

Rahoton na kasashen yankin Amurka, shi ne irinsa na farko da ya bada irin wannan shawarar a cikin kasashen.

Ya yi nuna da cewa ya kamata a rinka la'akari da masu ta'ammali da tabar wiwi a matsayin marasa lafiyar da za a kula da su, maimakon a hukunta su.

Rahoton ya ce gwamnatoci za su samu rarar kudade masu yawa da a yanzu ake amfani da su wajen yaki da shan tabar wiwi.

Sai dai rahoton bai samu goyon baya a kasashen yankin ba domin ya halatta miyaguyun kwayoyin da aka fi haramtawa wato hodar iblis ta Cocaine da kuma Heroin.