Gobara ta jefa mazauna garin Misau cikin zullumi

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Jama'ar garin Misau dake jihar Bauchi a arewacin Nijeriya na ci gaba da zama cikin zullumi da firgita sakamakon wata gobara mai daure kai wadda ta addabe su cikin 'yan kwanakin nan.

Gobarar dai ta lashe gidaje da dama, kuma ta fi kamari ne a unguwar Gwargeldi inda wata mata da abun ya shafa ta shaidawa BBC cewa suna cikin tashin hankali, kuma a filin Allah suke kwanan zaune.

Su dai mutanen na Misau sun bayyana cewa sun yi imanin aljanu ne ke cinna wutar, domin a cewarsu aljanun sun ma yi maganar cewa da ma yankin nasu ne, amma suka yi tafiya kimanin shekaru dari biyu da suka gabata, sai mutanen unguwar da lamarin ya shafa suka yi gine-gine a gidajen su aljanun, don haka mutanen su tashi su bar ma su wurinsu.

Sarkin garin na Misau, Alhaji Mahamadu Manga na uku, ya yi kira ga jama'a da su cigaba da addu'a da kuma sadaka ko Allah ya kawo saukin al'ammarin.