Sojojin Najeriya sun ce suna samun galaba

Sojojin Najeriya
Image caption An tura karin sojoji zuwa yankin na arewa maso gabas

Rundunar sojan Najeriya ta ce, ta sami galaba a kwana na biyu a hare-haren da take kaiwa a sansanonin kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojan Najeriya, Birgediya Janar Chris Olukolade ya ce sun samu sun lalata sansanonin 'yan ta'adda, a yankunan arewaci da kuma tsakiyar jahar Borno.

"Sojojin gwamnati sun hallaka masu tada kayar baya kimanin talatin, a gandun dajin Sambisa - duk dai a jahar ta Borno," a cewarsa.

Sai dai ba wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin sojojin.

Tun bayan da shugaban kasar ya kafa dokar ta baci a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe - saboda kazantar hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.

Rahotanni sun ce an tura kimanin sojoji 2,000 zuwa jihar ta Borno domin kwace wasu yankuna da hukumomi suka ce 'yan kungiyar ta Boko Haram na iko da su.

An kuma bayar da rahoton cewa an rufe kan iyakokin Najeriyar da kasashen Chadi, da Kamaru da Nijar ta bangaren jihohi ukun da dokar ta bacin ta shafa.

Karin bayani