Sojoji sun ce sun kashe 'yan Boko Haram 10 a Borno

Sojojin Najeriya
Image caption Wani wuri da sojojin Najeriya ke bincike

A wata sanarwa da ta fitar rundunar tsaro ta Najeriya ta ce ta kama masu tada kayar baya sittin da biyar a lokacin da suke kokarin shiga cikin Maiduguri daga sansanonin da ake artabu da su.

Rundunar ta ce ta kuma kwace motocin su 11 da adaidaita sahu 4 da kuma wayoyin tafi da gidanka 24. Sanarwar ta kuma ce, a yayin artabun da akayi a jiya a garin Gamboru, sojojin sun yi nasarar kashe masu tada kayar baya goma, tare da kwace makamai da dama a wurin su.

Sai dai kuma babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan batu.

A halin da ake ciki kuma, Kakakin rundunar tsaro ta hadin gwiwa a jihar Borno, Laftana kanar Sagir Musa ya fitar da wata sanarwa in da ya ce, domin tabbatar da gudanar da aikin su yadda ya kamata, an sanya dokar takaita zirga-zirga ta tsawon sa'oi 24 a wasu unguwanni na Maiduguri da ma kewaye da suka hada Gamboru da Mairi Kuwait da Bakin Kogi da Kasuwan shanu da kuma hanyar Baga.

Wannan al'ammari dai na zuwa ne yayinda wasu rahotanni ke cewa wasu mazauna garuruwan da sojoji suka fara kai farmaki sun fara barin gidajen su sakamakon artabun da ake tsakanin jami'an sojoji da kuma masu tada kayar baya inda suke komawa garuruwan da ke kan iyaka da kasar Kamaru da suka hadar da Gamborou Fotokol da Darak da Banki Amchige da kuma Kouseri.

Karin bayani