An tura karin sojoji 1,000 zuwa Adamawa

Sojojin Nigeria
Image caption Sojoji sun sha alwashin kakkabe masu tayar da kayar bayan

Rundunar sojin Najeriya ta tura karin dakaru zuwa Jihar Adamawa a ci gaba da aiwatar da dokar ta-bacin da aka kafa a jihar da sauran jihohin Borno da Yobe.

Kakakin rundunar sojin a Adamawa Laftanar Jaafaru Nuhu, ya ce karin dakaru 1,000 aka tura jihar - kuma a safiyar Litinin 150 daga cikinsu suka isa Yola babban birnin jihar.

Yawancin dakarun dai za su nufi yankunan da ake fama da tashin hankalin 'yan kungiyar Boko Haram ne - musamman yankunan da ke da iyaka da kasar Kamaru.

Harwa yau rundunar sojin Najeriyar na ci gaba da farautar masu tayar da kayar bayan a jihar Borno, a rana ta shida ta farmakin da sojoji suka kaddamar a yankin na Arewa maso Gabas.

Amma rundunar sojin ta ce za ta yi afuwa ga dukkan 'yan bindigar da suka ajiye makamansu, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wata sanarwa da sojin suka fitar, ta ce an kashe mayaka 14 na kungiyar ta Boko Haram, an kuma kama wasu 20, yayin da aka kashe sojojin gwamnati uku a gumurzun.

'Yan gudun hijira..

A wurin wata ganawa da ministocin Najeriya da jami'an Tarayyar Turai a birnin Brussels ranar Alhamis, Tarayyar ta gargadi Najeriya kan amfani da karfi fiye da kima.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama da Amurka, duka sun nuna damuwa kan zargin da ake yi wa sojojin Najeriya na cin zarafin fararen hula - zargin da sojin suka musanta.

Rahotanni daga jahar Diffa ta Nijar mai makwabtaka da Najeriya, sun ce wasu daruruwan mutane da suka hada da mata da kananan yara na kwarara zuwa yankin Bosso da ke cikin jahar.

Wasu daga cikin mutanen sun shaidawa BBC cewa sun gudo ne daga yankin Abadan da ke cikin jahar Borno a Najeriya, saboda fargabar irin abin da ka iya biyo baya, sakamakon karin dimbin jami'an tsaron da gwamnatin tarayya ta tura a yankin.

Sun ce yawansu ya kai dubu 2 zuwa dubu 3, kuma hukumomi da jama'ar garin na Bosso sun karbe su hannu biyu- biyu.

Karin bayani