Mutane hudu sun hallaka a wata Coci a Ghana

Shugaba John Mahama na Ghana
Image caption Shugaba John Mahama na Ghana

Mutane hudu ne suka mutu, wasu sha uku suka ji raunuka a wani turmutsutsi a cocin Evangelica a Ghana.

Lamarin ya auku ne a lokacin da mahalarta addu'o'i a cocin suka yi ta ruguguwar zuwa samun wani ruwa mai tsarki, a reshen cocin Synagogue Church of All Nations dake birnin Accra.

Rahotanni sun ce dubban jama'a ne suka halarci addu'o'in a cocin.

Wani mai wa'azi dan Najeriya, TB Joshua ne ya kafa cocin.

Ya janyo kace- nace kan ikirarin da ya yi cewa yana iya maganin cututtuka irinsu HIV da AIDS ko SIDA.

Karin bayani