Shugaba Morsi ya ce ba zai ba da kai ga masu garkuwa ba

Shugaba Morsi na Masar
Image caption Shugaba Morsi na Masar

Shugaban kasar Masar, Muhammad Morsi ya kawar da yuwuwar tattaunawa da wasu da suka sace wasu jami'an tsaron kasar su bakwai a yankin Sinai ranar Alhamis.

Ya yi wannan furuci ne bayan fitar wani video a intanet dake nuna wasu mutane bakwai da aka rufe ma fuskoki, wadanda suka ce ana garkuwa ne da su, suna rokon shugaban kasar ya sa baki.

Daya daga cikin mutanen, ya nemi shugaba Morsi da ya sako wasu fursunonin siyasa da ake tsare da su a yankin na Sinai, a matsayin musaya da su.

Wanda ya sa hoton videon dai ya boye sunansa.

Yankin na Sinai na kara zama makwantar rikici, tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak a 2011.