'Yan gudun hijira na kwarara cikin Nijar daga jihar Borno

Sojojin Najeriya a Maiduguri
Image caption Tura karin sojoji zuwa yankunan da aka kafa dokar ta baci ya tsorata jamaar yankunan

A jamhuriyar Nijar rahotanni daga jahar Diffa mai makwabtaka da Najeriya, sun ce wasu daruruwan mutane da suka hada da mata da kananan yara na kwarara zuwa yankin Bosso da ke cikin jahar.

Wasu daga cikin mutanen sun shaidawa BBC cewa sun gudo ne daga yankin Abadan da ke cikin jahar Borno a Najeriya, saboda fargabar irin abin da ka iya biyo baya, sakamakon karin dimbin jami'an tsaron da gwamnatin tarayya ta tura a yankin.

Sun ce yawansu ya kai dubu 2 zuwa dubu 3, kuma hukumomi da jama'ar garin na Bosso sun karbe su hannu biyu- biyu.

Gwamnan jihar Diffa, Kanal Manjo Mamadou Fode Camara ya shaidawa wakilinmu dake Yamai, Baro Arzika cewa galibin 'yan gudun hijirar 'yan Nijar da suka dade suna zaune a Najeriya, kuma tuni ya tura wata tawaga da ta kunshi jami'an gwamnati da na kungiyoyin agaji zuwa garin na Bosso, domin kiyasta halin da 'yan gudun hijirar ke ciki, da nufin kai mu su kayan agajin da suke bukata.

Jihohin Borno da Yobe da Adamawa ne dai gwamnatin ta Najeriya ta kafa dokar ta baci a cikinsu, a kokarin murkushe kungiyar da aka fi sani da Boko Haram, wadda ake dorawa alhakin galibin hare-haren da ake kaiwa a yankin.

Karin bayani