Sojojin Syria sun kai farmaki a Qusayr

Sojin Syria
Image caption Sojin Syria sun ce sun yiwa garin Qusayr kawanya

Rahotanni daga Syria na cewa dakarun gwamnati sun kaddamar da wani farmaki da nufin sake kwace garin Qusayr na yammacin kasar, inda suka shafe makonni suna yi wa 'yan tawaye kofar-rago.

Gidan talabijin na Syria ya ce sojojin gwamnati sun yi wa mayakan 'yan tawayen kawanya a garin,kuma sun ruguza wasu sansanonin 'yan tawayen a kudancin birnin.

Wasu masu fafutuka sun ce an kashe mutane ashirin a sakamakon mummunan barin wuta.

A halin da ake ciki kuma, shugaban kasar ta Syria, Bashar al-Assad , ya gargadi Amurka cewa yunkurin da take na shirya tattaunawar sulhu ba zai kawo karshen yakin basasar Syria ba.

A wata hira, da ba kasafai ya saba yi ba, da jaridar Clarin ta Argentina, Mr Assad ya nanata cewa ba shi da niyyar sauka daga mulki har sai 2014, lokacin da za a gudanar da sabon zaben shugaban kasa.

Amurka da Rasha na kokarin shirya taron sulhun ne a Geneva cikin watan Yuni, inda suke son hada wasu mukarraban gwamnatin shugaba Assad din da na 'yan tawayen dake kokarin kifar da shi.

Karin bayani