HukumominTunisia na takun saka da kungiyar Ansar al-Shari'a

Hargitsi a Tunisia
Image caption Hargitsi a Tunisia

'Yan sanda a Tunis, babban birnin Tunisia, sun yi amfani da barkonon tsohuwa a kan wasu masu zanga zanga dake jifa da duwatsu, na kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Ansar al-Shari'a, wadanda ke kokarin tattaruwa domin yin wani gangami da aka haramta.

An yi wani hargitsin a garin Kairouan dake tsakiyar kasar.

Ranar Larabar da ta wuce ne jam'iyyar Ennahda mai matsakaicin ra'ayin Islama dake jan ragamar gwamnatin Tunisiar ta bayyana cewar taron da kungiyar Ansar al-Shariar zata gudanar na shekara shekara, wanda ada aka shirya yi a Kairouan ba ya bisa ka'ida, domin ba ta nemi izini ba.

Sai dai kungiyar ta Ansar al-Sharia ta sha alwashin yin taron ko ana ha-maza-ha mata, inda ta bukaci magoya bayanta cewa yanzu su hallara a wajen birnin Tunis.