Iraq: Ana ci gaba da tashin hankali

Image caption Hare-haren bam suna ƙaruwa a Iraki

Fiye da mutane sittin sun hallaka a jerin wasu hare-haren bam a sassa daban-daban na kasar Iraki.

Kuma cikin 'yan makonnin nan an samu tashin hankali mafi muni cikin shekaru biyar a ƙasar.

Yawancin wadanda suka mutun 'yan Shi'a ne dake biranen Bagadaza da Basra.

A 'yan makonnin nan dai, hare-hare tsakanin 'yan Shia da mabiya Sunni a Irakin na dada ƙaruwa.