Sojin Najeriya 'sun kwace garuruwa daga Boko Haram'

MATAKAN TSARO A MAIDUGURI
Image caption MATAKAN TSARO A MAIDUGURI

Dakarun Najeriya sun ce, sun mamaye wasu yankuna a arewacin jahar Borno, bayan sun tarwatsa sansanonin 'yan kungiyar Boko Haram.

A makon jiya ne gwamnatin kasar ta kafa dokar ta-baci a jihohin Bornon, da Yobe da kuma Adamawa, masu fama da tashe tashen hankula.

Wata sanarwa da Rundunar sojin kasar ta fitar a ranar Litinin, ta ce sojojin na saduwa da mazauna yankunan suna basu tabbacin kare lafiyar su.

Rundunar tsaron Nijeriyar ta ce dakarun musamman sun kwace iko da Sabuwar Marte, da Hausari, da Krenoa, da Wulgo da Chikun Ngulalo, bayan sun rusa wasu sansanonin da sukace sun gano na wadanda suka kira 'yan ta'adda.

hedkwatar tsaron ta kuma yi ikirarin cewa 'Yan kungiyar ta boko Haram na tserewa suna shiga makwabtan kasashe irinsu Chadi da Nijar, kuma dakarun hadin gwiwa na kasashen dake kan iyaka na fuskantarsu.