Dakarun Najeriya za su saki wadanda ake zarginsu da ta'addanci

sojoji
Image caption Sojoji na sintiri a jihohin Borno, Yobe da Adamawa

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta soma sakin wasu daga cikin wadanda take tsare dasu bisa zargin hannu a cikin ayyukan ta'addanci.

Kakakin rundunar, Birgadier Janar Chris Olukolade a cikin wata sanarwa, ya ce matakin sakin mutanen, na daga cikin yinkurin gwamnatin tarayya na kokarin sasantawa da 'yan kungiyar Boko Haram, kamar yadda da kwamitin da aka kafa don tattaunawa da 'yan kungiyar ya bukata.

A cewar sanarwar, duka matan da ake tsare dasu bisa zargin hannu cikin ayyukan ta'addanci za su soma walwala.

Tuni dai gwamnatin tarayyar ta baiwa hukumar tsaro ta hadin gwiwa da cibiyoyinta dake inda lamarin ya shafa su soma aiwatar da umurnin data bayar.

Wadanda za a sakin, za a mika su wajen gwamnonin jihohinsu ne, inda za ayi musu horon gyaran halinka, kafin su koma cikin al'umma.

A ranar Litinin ne, rundunar sojin ta ce ta kama wasu 'yan ta'adda su 120 a lokacin da suke kokarin binne wani kwamandansu da sojoji suka kashe a garin Maiduguri.

Karin bayani