Majalisun dokoki sun amince da dokar ta baci

majalisa
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

A Najeriya majalissun dokokin dattawan kasar sun amince da bukatar da shugaba, Goodluck Jnathan ya gabatar masu domin amincewa da dokar ta bacin da aka sanya a jihohi uku na arewa maso gabashin kasar dake fama da kalubalen tsaro mai nasaba da kungiyar da ake kira Boko Haram.

'Yan majalisar dattijai da na wakilai sun amince da kudurin aza dokar taba cin a jihohin Adamawa, da Borno da kuma Yobe, inda tuni dakarun Najeriya ke cigaba da abinda suka kira kokarin kawar da 'yan kungiyar nan da ake kira Boko Haram.

Rahotanni daga kasar na cewar hukumomin soja a jihar Adawawa sun sassauta dokar hana zirga-zirga da sa'a guda, dokar da suka kafa tun bayan ayyana dokar ta baci a cikin jihar.

Wata sanarwa da kakakin soja a jihar, Laftanar Ja'afaru Nuhu ya sanyawa hannu ta ce, yanzu dai dokar zata soma aiki ne daga karfe bakwai 7: na maraice, zuwa karfe zuwa karfe shidda na safe.

Karin bayani