Sojoji sun yi 'gagarumin kamu a Maiduguri'

MATAKAN TSARO A MAIDUGURI
Image caption Sojoji sun ce suna samun nasara a farmakin da suke kaiwa

Rundunar sojin Nigeria ta ce ta kame wasu gungun 'yan gwagwarmaya 120 a lokacin da suke kokarin binne wani kwamandansu da sojoji suka kashe a garin Maiduguri.

Sojojin sun kara da cewa sun sake kwace wasu yankuna biyar daga hannun masu tayar da kayar bayan.

Sai dai kawo yanzu babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.

Mako guda kenan tun bayan da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yayi shelar kafa dokar ta baci a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.

Wannan ne ya sa dakarun kasar kaddamar da hari ta hanyar amfani da jiragen yaki da kuma sojojin kasa a wasu yankunan jihar Borno.

Kare hakkin bil'dama

Hedkwatar tsaron ta kuma yi ikirarin cewa 'Yan kungiyar ta boko Haram na tserewa suna shiga makwabtan kasashe irinsu Chadi da Nijar, kuma dakarun hadin gwiwa na kasashen dake kan iyaka na fuskantarsu.

Kimanin mutane 3,000 ne aka akshe tun bayan da Boko Haram suka fara kaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro a arewacin Najeriya.

Sai dai kungiyar ta sha kai hari kan fararen hula da kuma wuraren ibada.

Wani batu da yake jan hankalin mutane shi ne na kare hakkin fararen hula, ganin cewa ana zargin sojojin da take hakkin bil'adama.

Amma sojojin sun sha musanta hakan, a yanzu ma sun ce suna ganawa da mazauna yankunan don basu tabbacin kare lafiyar su.

Karin bayani