Koriya ta Arewa ta yi amai ta lashe

China
Image caption Dangantaka ta dan yi tsami tsakanin China da Koriya ta Arewa

Koriya ta arewa ta saki wani jirgin masunta 'yan China da ta kama makonni biyu da suka gabata, bayan da a baya tace sai an biya kudi za ta sake shi.

Kafar yada labaran kasar Sin ta ce duka wadanda suke cikin jirgin su 16 suna cikin koshin lafiya kuma suna kan hanyarsu ta komawa gida.

Koriya ta Arewa ta bukaci a biya ta kusan dala miliyan daya domin ta saki jirgin.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ba a biya ko kwabo ba.

Zaman dar-dar tsakanin Koriya ta Arewa da China wadda itace babbar mai mara mata baya ya karu, bisa batun shirin gwajin makamin nukiliyar koriya ta Arewar.