Mahaukaciyar guguwa ta afkawa Oklahoma

Mahaukaciyar guguwa ta afkawa Oklahoma
Image caption Ana sa ran adadin wadanda suka mutu zai karu

Akalla mutane 91 ne suka mutu bayan da wata guguwa ta ratsa da wajen birnin Oklahoma na Amurka, inda ake sa ran adadin wadanda suka mutun zai karu, a cewar ofishin babban jami'in lafiya na birnin.

Kimanin mutane 120 ne, ciki harda yara 70, ake yi wa magani saboda raunukan da suka samu a asibitocin da ke kewayen Moore.

Guguwar wacce ta afkawa birnin a ranar Litinin da yamma ta haifar da wuta - ta zubar da gidaje, sannan ta rusa makarantu.

Za a ci gaba da aikin bincike da kuma kai dauki har cikin dare, a cewar jami'ai.

Shugaba Obama ya bayyana lamarin da cewa wani bala'i ne.

Guguwar ta fi shafar yankin Moore, mai mutane 55,000, da ke wajen Kudancin birnin Oklahoma, sannan ta tsaya a wurin har kusan mintina 45.

Wannan bangare na Amurka ya fi kowanne fama da irin matsalar ta yanayi.

Ko a shekara ta 1999, dubban gidaje ne suka rushe lokacin da irin wannan guguwar da ba a taba ganin irinta ba a tarihi ta afkawa yankin.

Karin bayani