Gwamnatin Borno ta yi na'am da sakin 'yan Boko Haram

Image caption Gwamnatin Najeriya za ta saki wadanda ake zargi da ta'addanci

Gwamnatin Jahar Borno ta ce ta yi farin ciki da sanarwar da hedikwatar tsaron Najeriya ta bayar cewar ta umarci rundunar sojojin kasar da ta saki wasu da ake tsare da su bisa zargin aikata ta'addanci.

Gwamnatin Borno ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da ta aikewa yan jaridu.

Mutanen da za a saki dai sun hada dukkanin matan da ake tsare da su, bisa zargin cewar yan kungiyar nan ce ta Jama'atu Ahlus Sunna Lid'dawati wal Jihad da ake kira Boko Haram.

Tun farko dai Shugaban kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa don sasantawa da 'yan kungiyar Boko Haram ya ce matakin da gwamnatin ta dauka na sakin wadanda ake tsare da su bisa zargin ta'addanci zai taimaka wajen yin sulhu da 'yan kugiyar.

Alhaji Tanimu Turaki ya shaidawa BBC cewa wannan mataki ya nuna cewa gwamnati da gaske take yi wajen sasantawa da 'yan kugiyar ta Boko Haram.

Kwamitin da yake jagoranta ne ya bayar da shawarar sakin 'yan kungiyar ta Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal-Jihad da ake tsare da su.

A cewarsa, ''Duk [mutum] mai hankali idan ya kalli wannan shawara da muka bayar da kuma amincewa da wannan shawara da gwamnati ta yi, [zai ga] alama ce ta son daidaitawa. Su ['yan Boko Haram] suna nuna damuwarsu a kan a saki mata da yara, to ga shi gwamnati ta fara daukar matakin yin abin da suke nema''.

Ranar Talata ne dai rundunar sojin Najeriya ta ce za ta fara sakin wadansu daga cikin wadanda take tsare da su bisa zargin suna da hannu a ayyukan ta'addanci.

Karin bayani