Nijar: Mutane 19 sun mutu a harin Agades

Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou
Image caption Gwamnatin Nijar na zargin kungiyoyi masu alaka da Al-Ka'ida da kai hare-haren

Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Nijar, Abdou Labo, ya shaida wa BBC cewa mutane 19 ne, ciki har da sojoji 18, suka rasa rayukansu a harin kunar-bakin-waken da aka kai wani barikin soji da ke birnin Agades.

An kashe hudu daga cikin 'yan kunar-bakin-waken, yayinda wani na biyar ya yi garkuwa da jami'an soji hudu a barikin.

A hari na biyu kuma a garin Arlit, ministan ya tabbatar da cewa mutane 50 sun jikkata.

An kai harin ne dai a kan wata mahakar ma'adinai ta kamfanin Areva na Faransa. Wadanda suka kai harin su biyu sun mutu.

Ministan ya ce ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren, amma yana zargin kungiyoyin mayaka masu alaka da kungiyar Al-Ka'ida.

Karin bayani