An kai harin bom a Agadez na jamhuriyar Nijar

Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou
Image caption Bama baman sun tashi ne kusan lokaci guda

Rahotanni daga birnin Agadez na jamhuriyar Nijar na cewa wani mutum da ake kyautata zaton dan kunar-bakin-wake ne ya tashi bom a wani barikin soji da ke birnin.

A can birnin Arlit ma, rahotanni na cewa wasu bama bamai sun tashi a kamfanin Somair mai hakar ma'adanin uranium.

Rahotannin na cewa mutumin da ya tayar da bom a Agadez ya rasa ransa yayin da mutane biyu suka jikkata.

Gwamnan jihar Agadez, Kanal Garba Maccido, ya tabbatarwa BBC da aukuwar lamarin, sai dai ya ce ba zai karin bayani ba sai anjima.

Tashin bama-baman ya faru ne da misalin karfe biyar na safiyar ranar Alhamis, kuma sun tashi ne kusan lokaci guda.

Karin bayani