Ban ki moon yana ziyara a Goma

Ban ki moon
Image caption Ban Ki moon ya ce za a dawo da zaman lafiya a Congo

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin duniya, Ban Ki- moon, ya shaidawa BBC cewar tabbas dakarun samar da da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya, da za a tura a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, za su kare fararen hula , su kuma samar da zaman lafiya a yankin da yaki ya dai-dai-ta.

Mr Ban wanda ke ziyartar birnin Goma, ya ce sojoji dubu uku ne za a tura gabashin Jumhuriyar Demokradiyar Congo don kawo karshen zubar da jini.

Yankin na Gabashin Congo dai ya dadfe yana fama da tashin hankali tsakanin sojojin gwamnati da mayakan kungiyoyin daban-daban dakle dauke da makamai.

A halin da ake ciki kuma, daya daga cikin kungiyoyin dake da hannu a fada na baya-bayan nan, wato M23, ta yi shelar tsagaita wuta saboda ziyarar ta Ban Ki Moon.

Karin bayani