Cameron ya yi Allah-wadai da kisan wani soja

David Cameron
Image caption Mr Cameron ya jaddada cewa za su murkushe ta'addanci

Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron, ya yi Allah-wadai da mutanen nan biyu wadanda a ranar Laraba suka daddatse wani soja har sai da rai ya yi halinsa a London, yana mai cewa sun ci mutuncin addinin Musulunci.

A lokacin da suke aika-aikar, mutanen biyu suna ta fadin "Allahu Akbar".

Firayim Ministan na Birtaniya ya jaddada cewa, za su murkushe 'yan ta'adda.

A yanzu mutanen biyu suna can kwance a asibiti, bayan 'yan sanda sun harbe su a jiyan.

Mista Cameron ya katse ziyarar da yake yi a Faransa ne inda ya koma gida Burtaniya a yau saboda aukuwar lamarin da mahukunta suka bayyana da cewa harin ta'addanci ne.

Mutane da dama ne dai suka tur da aukuwar wannan lamari, cikinsu har da al'umar musulmi da ke Burtaniya.

Shugaban kungiyar the Ramadhan Foundation, Mohammed Shafiq, ya ce harin da aka kai ba shi da alaka da musulinci.

Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a barikokin soja a duk fadin London, kuma an girke 'yan sanda fiye da dubu daya a birnin inda suke karin sintiri a wuraren ibada..

Karin bayani