Burtaniya: Gwamnati ta kare jami'an tsaro

Ginin Majalisar Dokokin Burtaniya
Image caption Majalisar Dokokin Burtaniya ta fara bincike a kan hakikanin abin da jami'an tsaro suka sani

Gwamnatin Burtaniya ta kare hukumomin tsaro daga sukar da ake yi musu saboda yadda suka kasa gane alamun da ka iya taimaka musu su hana kisan wani soja a wani titin birnin London ranar Laraba.

A baya dai hukumar binciken laifuffuka ta MI5 ta taba bincike a kan mutane biyu masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci wadanda aka kama a wurin da al'amarin ya faru, amma aka daina sa ido a kansu.

Wani babban jami'in gwamnati, Minista Eric Pickles, ya ce abu ne da ba zai yiwu ba a sa ido a kan kowa da kowa a ko wanne lokaci; kuma a cikin duk al'ummar da ke da 'yanci za a iya samun daidaikun mutane masu son tayar da zaune tsaye.

Majalisar Dokokin Burtaniya ta fara gudanar da bincike a kan hakikanin abin da hukumomin tsaron suka sani dangane da mutanen biyu, Michael Adebolajo da Michael Adebowale.

Duk su biyun dai haifaffun Burtaniya ne 'yan asalin Afirka.

Tsohon shugaban hukumar ta MI5, Richard Barret, ya shaida wa BBC cewa yana da muhimmanci a rika sa ido a kan mutanen da suka taba shiga hannun hukumar.

A cewarsa, "Ina ganin idan har jami'an tsaron sun koyi darasi, kamata ya yi a ce ana sa ido a kan take-taken duk wani wanda ya taba shiga hannunsu''.

Image caption Taswirar unguwar Woolwich ta birnin London mai nuna titin da aka kai harin

Karin bayani