Ana bincike a kan kisan da aka yi a Burtaniya

Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron
Image caption Firayim Minista David Cameron ya katse wata ziyara da yake yi a Faransa bayan faruwar lamarin

A Burtaniya, hukumomi na cigaba da bincike game da kisan gillar da aka yi wa wani soja a unguwar Woolwich da ke birnin London a ranar Laraba.

Jami'an tsaro na ci gaba da cikakken bincike na aikin ta'addanci a kan mutanen biyu [Michael Adebolajo da Michael Adebowale] wadanda ake zargi—dukkansu haifaffun Burtaniya ne 'yan asalin Afirka.

Hukumar leken asiri ta Burtaniya, MI5 ta taba tuhumar mutanen biyu, wadanda aka ce sun shiga addinin Musulunci a wani lokaci a baya, amma ba ta saka su cikin mutanen da ake sa ido a kansu ba.

Tsohon shugaban hukumar leken asirin, Richard Barret, ya shaida wa BBC cewa yana da muhimmanci a rinka sa ido a kan mutanen da suka taba shiga hannun hukumar.

A cewarsa, "Ina ganin idan har jami'an tsaron sun koyi darasi, kamata ya yi a ce ana sa ido a kan take-taken duk wani wanda ya taba shiga hannunsu''.

Majalisar Dokokin Burtaniya ta ce ta fara gudanar da bincike a kan abin da jami'an tsaro suka sani game da mutanen, da kuma dalilin da ya sanya ba a saka su a sahun wadanda ake sa ido a kansu ba.

Karin bayani