Kisan 'yan Iraki: Kotu ta nemi a yi sabon bincike

Image caption Iraki tana ci gaba da fuskantar tashin hankali

Alƙalai a babbar kotu a London sun yi ƙiran a sake wani sabon tsari a kan binciken zargin cewar, dakarun Birtaniya sun azabtar da fararen hula a ƙasar Iraki, lokacin mamayen da aka yiwa ƙasar a shekara ta 2003.

Lauyoyi masu kare hakkokin jama'a dake wakiltar fararen hula 'yan kasar Iraqi su ɗari da tamanin suna so ne a gudanar da bincike a bainar jama'a dangane da zargin cin zarafi da ma kisan fararen hula 'yan ƙasar Iraqi.

Sai dai kuma gwamnati ta ƙi amincewa da hakan, inda maimakon hakan ta kafa wani kwamiti a shekara ta 2010.

An ɗorawa kwamitin ne alhakin bankaɗo dukkan zarge-zargen azabtarwa da kuma kisan fararen hular Iraqi da dakarun Birtaniya suka aikata a Iraki.

Ita ma dai babbar kotun ba ta amince ayi wani bincike mai zurfi ba a bainar jama'a.