'An kuɓutar da waɗanda Boko Haram suka sace'

Image caption Dakarun Najeriya suna sintiri

Dakarun Najeriya sun yi ikirarin cewa, sun kuɓutar da mata uku da kuma yara ƙanana shida yayin samamen a sansanoni uku na 'yan ƙungiyar da ake kira Boko Haram a gandun dajin Sambisa, dake jihar Borno.

Sai dai kuma dakarun Najeriyar sun ce, har yanzu suna kokarin gano mace guda 'ya 'yanta biyu.

'Yan ƙungiyar ta Boko Haram ne dai suka sace matan da yaran yayin harin da suka kai barikin 'yan sanda na garin Bama a farkon wannan watan.

A wani hoton vidoyo da ƙungiyar Boko Haram ta fitar an nuna wasu mata da yara da suka ce, sun cafke su ne yayin harin da suka kai a garin Bama.

Tun bayan ayyana dokar ta-ɓaci a jihohi uku ne dai dakarun Najeriya suka ƙaddamar da farmaki a wuraren da ake zaton 'yan ƙungiyar Boko Haram sun kafa sansanoni.