''Dalilin da ya sanya aka kai wa Nijar hari''

Image caption Ya kamata 'yan Nijar su taimakawa jami'an tsaro da bayanai na 'yan ta'adda

Masana da masu sharhi sun bayyana cewa 'yan ta'adda sun kai wa Nijar hari ne saboda goyon bayan da kasar ta bayar wajen yaki da masu gwagwarmaya a kasar Mali.

Farfesa Bube na Maiwa, malami ne a Jami'ar Anta Diop da ke Dakar, babban birnin Senegal, kuma ya shaidawa BBC cewa 'yan ta'addan za su watsu zuwa kasashen da suka bai wa Faransa goyon baya a yakin da take yi.

A cewarsa, ''Kowa ya san irin goyon bayan da Nijar ta bai wa Faransa don yakar 'yan jihadi, don haka an kai mata hari ne don ramuwar gayya ga duk kasashen da suka goyi bayan Faransa''

Ya kara da cewa ya kamata duk kasashen da suka bai wa Faransa goyon baya su shirya don kaucewa harin 'yan ta'adda.

Image caption Taswirar Nijar mai nuna wiraren da aka kai hare-haren

Farfesa Bube na Maiwa ya ce dole 'yan Nijar su taimakawa jami'an tsaro don yakar 'yan ta'adda, yana mai cewa ya dole ne ['yan kasar ] su rika bayar da bayanai game da duk mutumin da ba su amince da take-takensa ba.

Karin bayani