Faransa na janye sojojinta daga Mali

Image caption Faransa ta yi amfani da jiragen yaki a Mali

Kasar Faransa za ta fara janye sojojin ta daga Mali nan da 'yan sa'oi masu zuwa.

Wani ayari na manyan motoci tamanin dauke da na'urori za su bar sansanin sojojin Faransa da ke Bamako, babban birnin kasar ta Mali zuwa birnin Abidjan na Ivory Coast.

Faransa ta tura sojoji dubu hudu ne zuwa kasar ta Mali a watan Janairu bayan gwamnatin Mali ta bukaci haka don fatattakar masu tayar da kayar-baya da masu kaifin kishin Islama da 'yan tawaye na Abzinawa.

Wasu daga cikin sojojin dai sun rigaya sun fice daga kasar.

Za a rage adadin sojojin na Faransa zuwa dubu biyu a watan Satumba, yayin da za a bar dubu daya kawai zuwa karshen wannan shekarar.

Karin bayani