Kerry ya nemi Najeriya ta kare fararen hula

Sakataren wajen Amurka
Image caption Sakataren wajen Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yayi kira ga hukumomin Nijeriya da su tabbatar cewa sojoji ba su ci zarafin fararen hula ba a hare haren da suke kaiwa kan 'yan kungiyar Boko Haram a arewacin kasar.

Mr Kerry wanda ke halartar taron cika shekaru hamsin na kafa kungiyar hada kan Afrika ya ce gwamnatin Amurka na bada cikakken goyon baya ga yunkurin gwamnatin Nijeriya na murkushe kungiyar Boko Haram da ta shafe shekaru hudu tana tayar da kayar-baya, amma ya ce ta'asar da wasu ke aikatawa bai bada damar wasu su kwata irinta ba.

Mr Kerry ya kuma yi kira ga hukumomin Nijeriyar da su dauki matakan samar da ababen more rayuwa ga jama'a, su kuma samar da karin guraben ayyukan yi, yana mai cewa talauci na daga cikin dalilan dake sa wasu zama masu tsauraran ra'ayoyi.

Karin bayani