Libya na barazana ga zaman lafiya - Issoufou

Nijar
Image caption Harin shi ne irinsa na farko da aka kai a kasar ta Nijar

Shugaban kasar Nijar Muhammadou Issoufou ya ce Libya ta zama wata cibiya ta samar da tashe-tashen hankula, tare da gargadin kasar za ta iya zama wata sabuwar kasar Somalia.

Mr Issoufou ya ce masu tada kayar bayan da suka kai hari a Nijar a ranar Alhamis sun zo ne daga kudancin kasar ta Libya.

Mutane 35 ne suka rasa rayukansu yayin harin a barikin sojoji da kuma wani kamfanin hakar ma'adinan Uranium mallakar kasar Faransa.

'Yan tawayen da ke fafutuka a kasar Mali ne dai suka dauki alhakin kai harin.

Sai dai shugaban ya ce za su duk iya kokarinsu wurin kare al'ummar kasar, tare da dakile duk wasu ayyukan ta'addanci.

Ya kuma bayyana wadanda suka kai harin da cewa 'ba Musulmai ba ne' saboda a cewarsa, Musulmi ba zai aikata hakan ba.

Karin bayani