Ana kokarin shawo kan matsalolin Afurka

Kwana guda bayan bukukuwan cika shekaru hamsin da kafa kungiyar hada kan kasashen Afrika, da yanzu ake kira Tarayyar Afrika, a birnin Addis Ababa, a yanzu shugabannin Afrikar sun dukufa ne wajen tattauna wasu daga cikin matsalolin dake addabar nahiyar.

Rikicin da ya-ki-ci ya-ki cinyewa a jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ne ya mamaye fara tattaunawar.

Daga nan sai tattaunawar ta koma kan wata shawara da za a gabatarwa kotun hukunta laifukkan yaki ta duniya da ta janye yunkurinta na gurfanar da sabon shugaban Kenya, da mataimakinsa a gaban kotun bisa zargin aikata laifukkan yaki kan Bila'adama.

Jami'an diplomasiyya na cewa kan shugabannin kasashen Afrikar ya rarrabu game da wannan batu.